YADDA WASU MASOYAN MAWAKI NURA M INUWA SUKA FARA ZANGA ZANGAR LUMANA AKAN JINKIRIN SAKIN ALBUM 2021
Assslmu alakum warahamatullah wabarakatutuhu bayan gaisuwa mai dafatan Kuna lafiya
Barkanmu da warhaka da sake saduwa da daku acikin wani sabon Shirin na Dandalin kannywood inda muke kawomuku labarai da rahotannin da suka shafi kannywood
Ayau muna dauke ne da wani abin mamaki da baa' taba jin irinsaba yadda asatin Nan akasamu wasu daga cikin masoyan shahararren mawaki watau nura m inuwa suka Fara zanga zanagar LUMANA a social media Akan rashin sakin album da mawakin yayi musu alkawari,
Kamar dai yadda mawakin da yayi suna aduniya abangaren wakokin soyayya yaba yi shine duk shekara Yana sakin album guda biyu ne
Sai dai ashekarar da ta ga bata 2020 bai saki Album din ba Ya kuma fito ya bawa dunbin masoyan nasa hakuri Kuma yace yayi Hakan saboda yayi dogon nazari akan abinda zai bawa masoyan nishadi
Kuma yayi alkawarin wannan shekarar zai saki album 2021
Hakan yasa dubun nan masoya da masu bibiyarsa suka damu yadda har Jan yawuce gashi mun shiga Feb Amma shiru kakeji kamar malam yaci shirwa
Me zakuce akan wadannan matasa Koda yake zamu iya cewa tsantsar kauna da soyayya ce Kuma wannan ya nuna cewa har yanzu tauraron mawakin na haskawa Keenan
Anan zamu dakata sai munji daga gareku zaku iya fadin ra'ayoyinku akan abinda muke post mun gode kuhuta lafiya.


0 Comments